Irmiya 41:1 - Littafi Mai Tsarki1 A watan bakwai sai Isma'ilu ɗan Netaniya, ɗan Elishama, na cikin zuriyar sarauta, ɗaya daga cikin ma'aikatan sarki, ya zo a wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa tare da mutum goma. Sa'ad da suke cin abinci tare a Mizfa, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 A wata na goma sha bakwai sai Ishmayel ɗan Netaniya, ɗan Elishama, wanda yake mai jinin sarauta yake kuma ɗaya daga cikin hafsoshin sarki, ya zo tare da mutum goma wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa. Yayinda suke ci tare a can, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa'an nan ya sallame shi.