Irmiya 40:5 - Littafi Mai Tsarki5 Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa'an nan ya sallame shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |