Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 40:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Yau na kwance ƙuƙumin da yake a wuyanka, idan ka ga ya fi maka kyau, ka zo mu tafi tare zuwa Babila, to, sai ka zo, zan lura da kai da kyau, amma idan ba ka ga haka ya yi maka daidai ba, to, kada ka bi ni. Ga dukan ƙasa shimfiɗe a gabanka, ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Amma yau ina ’yantar da kai daga sarƙoƙin da suke a hannuwanka. Zo mu tafi Babilon, in kana so, zan kuwa lura da kai; amma in ba ka so, kada ka zo. Ga shi, dukan ƙasar tana a gabanka; ka tafi duk inda ka so.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 40:4
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Abimelek kuwa ya ce, “Ga shi, ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda ya yi maka daɗi.”


Ba ƙasar duka tana gabanka ba? Sai ka ware daga gare ni. In ka ɗauki hagu in ɗauki dama, in kuwa ka ɗauki dama ni sai in ɗauki hagu.”


Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”


Sai Irmiya ya ce, “Ƙarya ce, ni ba gudu zuwa wurin Kaldiyawa nake yi ba.” Amma Irija bai yarda ba, sai ya kai shi wurin shugabanni.


Ya kewaye ni da garu don kada in tsere, Ya ɗaure ni da sarƙa mai nauyi.


Sai ka ce wa barorinka, ‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.’


Sa'an nan ya ce masa, “Da kuɗin, da mutanen duk an ba ka, ka yi yadda ka ga dama da su.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ