Irmiya 4:8 - Littafi Mai Tsarki8 Domin haka sai ku sa tufafin makoki, Ku yi makoki ku yi kuka, Gama fushin Ubangiji bai rabu da mu ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.