Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Zaki ya hauro daga cikin ruƙuƙinsa, Mai hallaka al'ummai ya kama hanya, Ya fito daga wurin zamansa don ya mai da ƙasarku kufai, Ya lalatar da biranenku, su zama kango, ba kowa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa; mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya. Ya bar wurinsa don yă lalace ƙasarku. Garuruwanku za su zama kufai babu mazauna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 4:7
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.


Zakuna suna ruri a kansa, Suna ruri da babbar murya. Sun lalatar da ƙasarsa, Garuruwansa sun lalace, Ba wanda yake zaune cikinsu.


Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.


An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko'ina kufai.


Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.


“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.


zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.


Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni?


Ni Ubangiji zan umarce su su komo zuwa wannan birni don su yi yaƙi da shi, su ci shi, su ƙone shi da wuta. Zan sa biranen Yahuza su zama kufai, ba masu zama a ciki.”


Haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan wuri da ka ce ya zama kufai, ba mutum ko dabba, wato a biranen Yahuza da titunan Urushalima, inda ba kowa, ba mutum ko dabba a ciki,


Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama'a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.


Ya rabu da wurin ɓuyarsa kamar zaki, Gama ƙasarsu ta zama marar amfani, Saboda takobin Ubangiji, da kuma zafin fushinsa.”


Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.


A zamanin Yehoyakim ne Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo wa Yahuza yaƙi, Yehoyakim kuwa ya zama baransa har shekara uku daga nan kuma ya tayar masa.


Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.


“Ni Ubangiji ina zuwa kamar zakin da yake fitowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya. Nan da nan zan sa su gudu daga gare ta. Sa'an nan zan naɗa mata wanda na zaɓa. Wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Wane shugaba zai yi gāba da ni?


“ ‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.


“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Urushalima tsibin kufai, Wurin zaman diloli, Zan kuma mai da biranen Yahuza kufai, inda ba kowa.”


A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai.


Da jin motsin mahayan dawakai da na maharba Kowane gari zai fashe. Waɗansu za su shiga kurama, Waɗansu kuma su hau kan duwatsu. Dukan birane za su fashe tas, Ba wanda zai zauna a cikinsu.


Zan shirya waɗanda za su hallaka ta. Kowannensu da makamansa, Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwan al'ul ɗinta, a jefa su a wuta.


“Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda yake zaune a cikinsu,


Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”


Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa.


“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir'auna, Sarkin Masar, ka ce, “ ‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al'ummai, Amma kai kada ne a cikin ruwa. Ka ɓullo cikin kogunanka, Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka, Ka ƙazantar da kogunansu.’


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.


Daga Dan, an ji firjin dawakai. Dakan ƙasar ta girgiza saboda haniniyar ingarmunsu. Sun zo su cinye ƙasar duk da abin da suke cikinta, Wato da birnin da mazauna cikinsa.”


Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza, “Kyanta kamar Gileyad take a gare ni, Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon. Duk da haka zan maishe ta hamada, Birnin da ba kowa ciki.


Ni wanda sunana Ubangiji Mai Runduna Sarki ne, Na rantse da raina, wani zai ɓullo, Kamar Tabor a cikin tsaunuka, Ko kuwa kamar Karmel a bakin teku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ