Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 4:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Da jin motsin mahayan dawakai da na maharba Kowane gari zai fashe. Waɗansu za su shiga kurama, Waɗansu kuma su hau kan duwatsu. Dukan birane za su fashe tas, Ba wanda zai zauna a cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 4:29
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zaki ya hauro daga cikin ruƙuƙinsa, Mai hallaka al'ummai ya kama hanya, Ya fito daga wurin zamansa don ya mai da ƙasarku kufai, Ya lalatar da biranenku, su zama kango, ba kowa.


Sa'an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kanmu,’ su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu.’


Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce, “Bugi ginshiƙan Haikali don shirayi duka yă girgiza. Farfasa su, su fāɗi a kan mutane! Sauran mutane kuwa, Zan kashe su a wurin yaƙi. Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.


Sai aka huda garun birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa'ad da Kaldiyawan take kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.


Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da take kan tudu.


Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.


Sa'ad da Isra'ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.


Zan sa jama'a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango.


Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi, Motsinsu kamar ƙugin teku ne. Suna haye a kan dawakai, A jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi Gāba da ke, ya 'yar Sihiyona.”


“Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ