Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 4:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Na duba, sai na ga ƙasa mai dausayi ta zama hamada, An mai da dukan biranenta kangwaye A gaban Ubangiji saboda zafin fushinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada; dukan garuruwanta sun zama kufai a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 4:26
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani, Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”


Amma mutane suna jin tsoronka! Wa zai iya tsayawa a gabanka Sa'ad da ka yi fushi?


Zan yi kuka in yi kururuwa saboda tsaunuka, Zan yi kuka saboda wuraren kiwo, Domin sun bushe sun zama marasa amfani. Ba wanda yake bi ta cikinsu. Ba a kuma jin kukan shanu, Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu sun tafi.


Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Zan sa muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya su ƙare a biranen Yahuza da titunan Urushalima, gama ƙasar za ta zama kufai.”


Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in.


Ubangiji ya wulakanta bagadensa, Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa. Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba, Suka yi sowa a Haikalin Ubangiji Kamar a ranar idi.


Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ