Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”
Zan yi kuka in yi kururuwa saboda tsaunuka, Zan yi kuka saboda wuraren kiwo, Domin sun bushe sun zama marasa amfani. Ba wanda yake bi ta cikinsu. Ba a kuma jin kukan shanu, Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu sun tafi.
Kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da bisashe, da dukan masu rarrafe, da dukan mutanen da suke duniya, za su yi makyarkyata a gabana. Za a jefar da duwatsu ƙasa, tsaunuka za su fādi, kowane bango zai rushe.