Irmiya 4:19 - Littafi Mai Tsarki19 Azaba! Ba zan iya daurewa da azaba ba! Zuciyata! Gabana yana faɗuwa da ƙarfi, Ba zan iya yin shiru ba, Gama na ji amon ƙaho da hargowar yaƙi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.