Irmiya 4:1 - Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji ya ce, “Ya mutanen Isra'ila, idan za ku juyo ku komo wurina, Idan kuka kawar da abubuwan banƙyama daga gabana, Kuka kuma bar yin shakka, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 “In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.