Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.
Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.