Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?
Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”
Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.
Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.”
Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.
Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa, “ ‘Aminanka sun ruɗe ka, Sun rinjaye ka. Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutse cikin laka, Sai suka rabu da kai.’