Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 38:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Amma idan ba ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila ba, to, za a ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa, za su ƙone shi da wuta. Kai kuma ba za ka tsira daga hannunsu ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Amma in ba ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon ba, za a ba da wannan birni ga Babiloniyawa za su kuma cinna mata wuta; kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 38:18
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama Ubangiji ya ce, hakika za a ba da wannan birni a hannun rundunar sojojin Sarkin Babila su ci shi.”


Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.


Sa'an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.


“Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”


Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta.


Sai Yekoniya Sarkin Yahuza ya ba da kansa ga Sarkin Babila shi da tsohuwarsa, da fādawansa da hakimansa. Sarkin Babila ya kama shi yana da shekara takwas da sarautar,


Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”


“ ‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.


Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima.


Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ