Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 37:7 - Littafi Mai Tsarki

7 “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 37:7
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idanunmu sun gaji Da zuba ido a banza don samun taimako, Mun zuba ido Ga al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.


Fir'auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa'ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa.


Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.”


“Ka tambayar mana Ubangiji, gama Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kawo mana yaƙi. Ko Ubangiji zai yi mana al'amuran nan nasa masu ban al'ajabi kamar yadda ya saba, ya sa Sarkin Babila ya janye, ya rabu da mu?”


Amma a kan Sarkin Yahuza, wanda ya aiko ku, ku tambayar masa Ubangiji, ku faɗa masa Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A kan maganar da ka ji,


Ba za su ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra'ila ba, gama Isra'ilawa za su tuna da laifin suka yi, suka nemi taimakon Masarawa. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”


Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya, Sai ku yi nan ku yi can? Masar za ta kunyata ku kamar yadda Assuriya ta yi.


Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.


Wace riba ka samu, har da ka tafi Masar, Don ka sha ruwan Kogin Nilu? Wace riba ka samu, har da ka tafi Assuriya, Don ka sha ruwan Kogin Yufiretis?


Da hannuwanku a kā za ku komo daga Masar don kunya. Gama waɗanda kuke dogara gare su, ni Ubangiji, na ƙi su, Ba za ku yi arziki tare da su ba.”


Wannan ita ce maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa Irmiya sa'ad da sarki Zadakiya ya aiki Fashur ɗan Malkiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, wurin Irmiya cewa,


Rundunar sojojin Fir'auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.


Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce,


A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.


Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir'auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa.


Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.


Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, ‘Macijin da ba ya yin kome.’ ”


Kana sa zuciya Masar za ta taimake ka, to, wannan ya zama kamar ka ɗauki kyauro ya zama sandan dogarawa, zai karye, ya yi wa hannunka sartse. Haka Sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara gare shi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ