Rundunar sojojin Fir'auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.
“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.
Zadakiya Sarkin Yahuza, ya sa shi a kurkuku, gama ya ce, “Don me kake yin annabci? Ka ce, Ubangiji ya ce, ga shi, zai ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa cinye shi da yaƙi.
“Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.