Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 37:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 37:3
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su.


cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’


haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama'ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma'aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa:


Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne mahaifinmu.’ Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka haife mu.’ Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, ‘Ka zo ka taimake mu.’


Sarki Yerobowam ya ce wa annabin, “In ka yarda ka yi roƙo ga Ubangiji Allahnka domina, ka yi mini addu'a don ya warkar da hannuna.” Annabi ya roƙi Ubangiji, sai hannun sarki ya komo daidai.


Sai saminu ya amsa ya ce, “Ku roƙar mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukar mini.”


Shefatiya ɗan Mattan, da Gedaliya ɗan Fashur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da Fashur ɗan Malkiya, suka ji maganar da Irmiya yake faɗa wa dukan mutane cewa,


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.


Suka ce wa Sama'ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”


Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.


Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.”


Ku roƙi Ubangiji ya tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”


Sai Firauna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya a jeji, sai dai kada ku tafi da nisa. Ku kuma yi mini addu'a.”


Sai Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa'an nan zai saki jama'ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.


Ubangiji ya ce mini, “Zan keɓe ka domin alheri, hakika zan sa abokan gaba su yi roƙo gare ka a lokacin bala'i da kuma lokacin damuwa.


“Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.


Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?” Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.”


Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama'a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ