Irmiya 37:1 - Littafi Mai Tsarki1 Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Nebukadnezzar sarkin Babilon ya naɗa Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda; ya yi mulki a madadin Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.