Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 36:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Mai yiwuwa ne idan mutanen Yahuza suka ji dukan masifar da na yi niyya in aukar musu da ita, za su bar mugayen ayyukansu don in gafarta musu muguntarsu da zunubinsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Wataƙila sa’ad da mutanen Yahuda suka ji game da kowace masifar da na shirya in auka musu, kowa ya juya daga muguwar hanyarsa; sa’an nan in gafarta musu muguntarsu da kuma zunubinsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 36:3
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

idan wannan al'umma da na yi magana a kanta, ta juyo, ta tuba daga mugayen ayyukanta, zan janye masifar da na yi niyyar aukar mata.


Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,


Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne.


Mai yiwuwa ne su ji, har kowa ya juyo ya bar muguwar hanyarsa. Ni ma sai in janye masifar da na yi niyyar aukar musu da ita, saboda mugayen ayyukansu.”


kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau,


Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.”


Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.


domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”


don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”


Na yi ta aiko muku da bayina annabawa, ina cewa, kowa ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara ayyukansa, kada ya bauta wa gumaka. Ta haka za ku zauna a ƙasa wadda na ba ku, ku da kakanninku, amma ba ku kasa kunne, ku ji ni ba.


Zan ba su zuciyar da za su sani ni ne Ubangiji. Za su kuwa zama jama'ata, ni kuwa zan zama Allahnsu, gama za su komo wurina da zuciya ɗaya.


Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, ‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.’


Sa'an nan Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”


Sa'an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau.


Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Wai don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’


Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.


Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’


Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’


Ku nemi Ubangiji, Dukanku masu tawali'u na duniya, Ku waɗanda kuke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali'u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.


Ni Ubangiji Allah, na ce, ina jin daɗin mutuwar mugu ne? Ban fi so ya bar mugun halinsa ya rayu ba?


Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”


Sa'an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”


Amma idan kun juyo wurina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, ko da yake an warsatsar da ku can nesa, zan tattaro ku, in kawo ku wurin da na zaɓa domin in sa sunana ya kahu a wurin.’


Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa'ida gare su da 'ya'yansu har abada.


Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni, Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ