Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 36:12 - Littafi Mai Tsarki

12 sai ya gangara gidan sarki, ya shiga ɗakin magatakarda, inda dukan shugabanni suke zaune, wato Elishama magatakarda, da Delaiya ɗan Shemaiya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemariya ɗan Shafan, da Zadakiya ɗan Hananiya, da dukan sarakuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 36:12
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan sai sarki Yehoyakim ya aiki waɗansu mutane zuwa Masar, wato Elnatan ɗan Akbor da waɗansu tare da shi.


Ko da yake Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su.


Sa'an nan ya umarci Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikaiya, da Shafan magatakarda, da Asaya baran sarki cewa,


A watan bakwai sai Isma'ilu ɗan Netaniya, ɗan Elishama, na cikin zuriyar sarauta, ɗaya daga cikin ma'aikatan sarki, ya zo a wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa tare da mutum goma. Sa'ad da suke cin abinci tare a Mizfa,


Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima.


Sai Hilkiya firist, da Ahikam, da Akbor, da Shafan, da Asaya suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, wato jikan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiye tufafi. A Urushalima take zaune a sabuwar unguwa. Suka kuwa yi magana da ita.


A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, wato jikan Meshullam, magatakarda, zuwa Haikalin Ubangiji, ya ce,


Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”


Sa'ad da sarakunan Yahuza suka ji waɗannan al'amura, sai suka fito daga gidan sarki zuwa Haikalin Ubangiji, suka zauna a bakin Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.


Amma Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bashe shi ga mutane don su kashe shi ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ