Irmiya 35:17 - Littafi Mai Tsarki17 Domin haka, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce zan kawo wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima masifar da na ce zan kawo musu, domin na yi musu magana, ba su ji ba, na kira su, ba su amsa ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 “Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.