Irmiya 35:14 - Littafi Mai Tsarki14 Umarnin da Yonadab ɗan Rekab ya yi wa 'ya'yansa, kada su sha ruwan inabi, sun kuwa kiyaye shi. Ba su taɓa shan ruwan inabi ba har wa yau, domin suna biyayya da umarnin kakansu. Ni kuwa na yi ta yi muku magana, amma ba ku kasa kunne gare ni ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.