Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 34:9 - Littafi Mai Tsarki

9 cewa kowa ya saki bayinsa, mata da maza, waɗanda suke Yahudawa. Kada kowa ya riƙe bawa wanda yake Bayahude, ɗan'uwansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Kowa ya ’yantar da bayinsa da suke Ibraniyawa, maza da mata; kada kowa ya riƙe bawa wanda yake mutumin Yahuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 34:9
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra'ila ne, na kabilar Biliyaminu, Ba'ibrane ɗan Ibraniyawa, bisa ga Shari'a kuwa ni Bafarisiye ne,


In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra'ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.


Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma 'yan'uwanku kuke yi wa!


Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama'a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai 'yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka 'yantar da su.


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “A wannan rana zan karya karkiya da take a wuyansu, in cire musu ƙangi, ba kuma za su ƙara zama bayin baƙi ba.


Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa'an nan al'ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.


Al'ummai da yawa da manyan sarakuna za su bautar da su, ni kuwa zan yi musu sakayya bisa ga ayyukan hannuwansu.’ ”


Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”


Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”


Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma'anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin,


“Idan aka sayar muku da Ba'ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku 'yantar da shi.


Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’


Sa'ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne.”


Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”


Sai wani da ya tsere, ya zo ya faɗa wa Abram Ba'ibrane wanda yake zaune wajen itatuwan oak na Mamre, Ba'amore, ɗan'uwan Eshkol da Aner, waɗanda suke abuta da Abram.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ