Irmiya 34:3 - Littafi Mai Tsarki3 Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’