23 Ubangiji kuma ya ce wa Irmiya,
23 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”
“Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba.