Irmiya 33:16 - Littafi Mai Tsarki16 A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 A kwanakin nan zan ceci Yahuda Urushalima kuma za tă zauna lafiya. Sunan da za a kira ta shi ne, Ubangiji Adalcinmu.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.