Irmiya 33:13 - Littafi Mai Tsarki13 A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”