Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 33:11 - Littafi Mai Tsarki

11 za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 33:11
47 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce!


Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu, Su raira waƙoƙin murna, Su faɗi dukan abin da ya yi!


Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce!


Ku yabi Ubangiji! Ku yi wa Ubangiji godiya, gama nagari ne shi, Ƙaunarsa madawwamiya ce.


To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.


Su waɗanda ka fansa Za su kai Urushalima da farin ciki, Da waƙa, da sowa ta murna. Za su yi ta murna har abada, Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.


Hezekiya kuwa ya amsa ya ce, “Yanzu dai kun tsarkake kanku ga Ubangiji. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a Haikalin Ubangiji.” Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, dukan waɗanda suka yi niyya kuwa suka kawo hadayu na ƙonawa.


Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa'ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Gama shi nagari ne, Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.” Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,


Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba, Don attajiranki, dā su ne ƙusoshin duniya, An kuma yaudari dukkan al'ummai da sihirinki.


Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.


Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa, Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!


“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama'ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.


Ki raira waƙa da ƙarfi, ya ke Sihiyona! Ki ta da murya, ya Isra'ila! Ki yi murna, ki yi farin ciki, Ya ke Urushalima!


Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā.


Zan sa muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya su ƙare a biranen Yahuza da titunan Urushalima, gama ƙasar za ta zama kufai.”


Ku ɓarke da sowar murna, Ku kufan Urushalima! Ubangiji ya ta'azantar da jama'arsa, Ya fanshi birninsa.


Zan miƙa maka hadaya ta godiya, Zan yi addu'ata a gare ka.


Sa'ad da dukan Isra'ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa.


Sa'an nan mutanen Ifraimu za su zama kamar ƙarfafan jarumawa, Za su yi farin ciki kamar sun sha ruwan inabi, 'Ya'yansu za su gani su yi murna, Zukatansu za su yi murna da Ubangiji.


Wane irin kyau da bansha'awa alherinsa yake! Hatsi zai sa samari su yi murna. Sabon ruwan inabi kuma zai sa 'yan mata su yi farin ciki.


Amma ni zan raira yabbai gare ka, Zan miƙa maka sadaka, Zan cika wa'adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.”


sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”


Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.


Gama ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan sa muryar murna, da ta farin ciki, da ta ango, da ta amarya, su ƙare a wurin nan a idonka da zamaninka.


Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.


Sai jama'a duka suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci. Suka yi murna ƙwarai domin sun fahimta dokokin da aka karanta musu.


Suka kuma kiyaye idin abinci marar yisti kwana bakwai da murna, gama Ubangiji ya sa su yi murna, ya kuma juyo da zuciyar Sarkin Assuriya wajensu, saboda haka ya taimake su da aikin Haikalin Allah, Allah na Isra'ila.


“Zan ji juyayi a kan Sihiyona, Da dukan masu zama a kufanta. Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu, Kamar lambun da na dasa a Aidan. Murna da farin ciki za su kasance a can, Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.


Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce, “Ku yi godiya ga Ubangiji, Saboda madawwamiyar ƙaunarsa Tabbatacciya ce har abada.”


Za su kai Urushalima da murna, Suna raira waƙa suna sowa don murna. Za su yi farin ciki har abada, Ba damuwa da ɓacin rai har abada.


Mutane za su zo daga biranen Yahuza da wuraren da yake kewaye da Urushalima, daga ƙasar Biliyaminu, da ta Shefela, da ta ƙasar tuddai, da kuma ta Negeb, suna kawo hadayu na ƙonawa da sadakoki, da hadayu na sha, da na turare, za su kuma kawo hadayu na godiya a Haikalin Ubangiji.


Daga cikinsu za a ji waƙoƙin godiya. Da muryoyin masu murna. Zai riɓaɓɓanya su, ba za su zama kaɗan ba, Zan kuwa ɗaukaka su, ba za a ƙasƙantar da su ba.


Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”


Ubangiji mai alheri ne, Shi mafaka ne a ranar wahala. Ya san waɗanda suke fakewa a gare shi.


Ka ƙaunace mu da madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji, Ka taimake mu da cetonka.


Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi, Yakan sa wa jama'arki albarka.


Waɗanda suke tsaron birni suna sowa, Suna sowa tare saboda murna! Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!


Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’ ”


Gama kwanaki suna zuwa sa'ad da zan komo da mutanena, wato Isra'ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,’ ni Ubangiji na faɗa.”


Zan komo da mutanena ƙasarsu, Za su giggina biranensu da suka rurrushe, Su zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi, su sha ruwan inabin. Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ