Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 32:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Sa’an nan, kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa, sai ga Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina ya zo wurina a sansanin matsara ya ce, ‘Saya filina a Anatot a yankin Benyamin. Da yake hakkinka ne ka fanshe shi ka kuma mallake shi, ka sayo shi wa kanka.’ “Sai na gane cewa wannan maganar Ubangiji ce;

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 32:8
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”


A lokacin nan kuwa sojojin Sarkin Babila sun kewaye Urushalima da yaƙi, annabi Irmiya kuwa yana a tsare a gidan waƙafi, a fādar Sarkin Yahuza.


Ubangiji ya sāke yin magana da Irmiya sa'ad da yake a kulle a gidan waƙafi.


Mikaiya ya ce masa, “A ran nan za ka gani, ka kuma gudu ka shiga har ƙurewar ɗaki don ka ɓuya.”


Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka.


Da haka aka karya alkawarina a wannan rana. Masu tumakin kore suna tsaye suna kallon abin da na yi, sai suka gane lalle wannan maganar Ubangiji ce.


Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.


Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.”


Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,


Duk da haka ya Ubangiji Allah, ka ce mini, ‘Sayi gonar da kuɗi, a gaban shaidu, ko da yake an ba da birnin a hannun Kaldiyawa.’ ”


sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi.


Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa'an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ