Irmiya 32:44 - Littafi Mai Tsarki44 Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202044 Za a sayi filaye da azurfa, a kuma sa hannu a takardan ciniki, a liƙe a kuma shaida a yankin Benyamin, a ƙauyukan kewayen Urushalima, a garuruwan Yahuda da kuma a garuruwan ƙasar tudu, na yammancin gindin dutse da na Negeb, domin zan maido da wadatarsu, in ji Ubangiji.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”