Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 32:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Zan ji daɗin yi musu alheri. Zan dasa su a wannan ƙasa da aminci da zuciya ɗaya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Zan yi farin ciki a yin musu alheri, tabbatacce zan su dasa a wannan ƙasa da dukan zuciyata da dukan raina.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 32:41
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan lura da su da kyau, in kuma komo da su a wannan ƙasa. Zan gina su, ba zan rushe su ba. Zan kafa su, ba zan tumɓuke su ba.


Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne. Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke. Zai sabunta ki da ƙaunarsa. Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.


Zan dasa su a ƙasar da na ba su, Ba kuwa za a ƙara tumɓuke su ba.” Ubangiji Allahnku ne ya faɗa.


Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa, Za ku yi murna tare, Kamar murnar amarya da ango.


Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama'arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.


Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa.


A duk kuma lokacin da na ce zan gina, in kafa wata al'umma, ko wani mulki,


Ubangiji Allahnku zai arzuta dukan aikin hannuwanku ƙwarai, ya kuma arzutar da 'ya'yanku da 'ya'yan shanu, da amfanin gona, gama Ubangiji zai ji daɗi ya arzuta ku kuma yadda ya ji daɗin kakanninku,


Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, haka nan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.


Ka fito da kurangar inabi daga cikin Masar, Ka kori sauran al'umma, Ka dasa kurangar a ƙasarsu.


Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba, Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.” Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.” Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,” Domin Ubangiji ya ji daɗinki, Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.


Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne.


Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai, Za su kuwa mallaki ƙasar har abada. Ni na dasa su, ni na yi su Domin su bayyana girmana ga duka.


Sa'an nan al'umman da suka ragu kewaye da ku za su sani, ni Ubangiji na sāke gina rusassun wuraren da suka zama kufai. Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”


Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila, Isra'ila za ta yi fure kamar lili, Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ