Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 32:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Zan yi madawwamin alkawari da su. Ba zan taɓa barin aikata musu alheri ba, zan kuma iza su su ji tsorona, don kada su ƙara juya daga gare ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 32:40
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi.


Zan ba su zuciyar da za su sani ni ne Ubangiji. Za su kuwa zama jama'ata, ni kuwa zan zama Allahnsu, gama za su komo wurina da zuciya ɗaya.


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


Ba kuma zan ƙara kawar da fuskata daga gare su ba, sa'ad da na saukar da Ruhuna a kan jama'ar Isra'ila, ni Ubangiji na faɗa.”


“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.


Za su tambayi hanyar Sihiyona, sa'an nan su bi ta, suna cewa, ‘Bari mu haɗa kanmu don mu yi madawwamin alkawari da Ubangiji, alkawari wanda ba za a manta da shi ba.’


Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,


Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir, Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.’


Amma shi da yake madawwami ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani.


Saboda haka tun alkawarin shiga inuwarsa tana nan, sai mu yi tsananin kula, kada ya zamana waninku ya kāsa shiga.


Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunar aikin gaskiya, Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi. Da aminci zan ba mutanena lada, In yi madawwamin alkawari, da su.


Jama'ar sun ƙazantar da duniya da suka keta dokokin Allah, suka ta da alkawarin da ya yi don ya dawwama.


Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”


Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”


Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.


Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!


Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka'idodina.


Ko da yake al'ummai suna bin gumakansu, Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ