27 “Ni ne Ubangiji Allah na dukan 'yan adam, ba abin da ya fi ƙarfina.
27 “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ’yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni?
Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”
“Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.
Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu,
tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.
Saboda kakan amsa addu'o'i, Dukan mutane za su zo wurinka.
Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”
“Bari Ubangiji Allah na ruhohin dukan 'yan adam ya shugabantar da mutum a kan taron jama'ar,
Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”
Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”
Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji, zai kuma ba da Mowabawa a hannunku.
Ubangiji kuwa ya ce wa Irmiya,
“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”
“Idan abin nan ya zama mawuyaci ga sauran jama'a a kwanakin nan, zai zama mawuyacin abu ne a gare ni?
Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”