na ba Baruk, ɗan Neriya, ɗan Ma'aseya, a gaban Hanamel, ɗan kawuna, da gaban shaidun da suka sa hannun a takardar shaidar sayen, da gaban dukan Yahudawa waɗanda suke zaune a gidan waƙafi.
“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ka ɗauki waɗannan takardun shaida, wadda aka liƙe da wadda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tukunyar ƙasa domin kada su lalace.’