Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 32:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a shekara ta goma ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza. A lokacin kuwa Nebukadnezzar yana da shekara goma sha takwas da sarauta a Babila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji a shekara ta goma ta Zedekiya sarkin Yahuda, wanda ya kasance shekara ta goma sha takwas ta Nebukadnezzar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 32:1
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana a kan dukan mutanen Yahuza. A shekarar da Nebukadnezzar ya ci sarautar Babila,


Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.


Wannan ita ce maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa Irmiya sa'ad da sarki Zadakiya ya aiki Fashur ɗan Malkiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, wurin Irmiya cewa,


A farkon sarautar Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana.


Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta.


A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima ɗari takwas da talatin da biyu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ