Irmiya 31:9 - Littafi Mai Tsarki9 Da kuka za su komo. Da ta'aziyya zan bishe su, in komar da su, Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan ruwa, A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba za su yi tuntuɓe ba. Gama ni uba ne ga Isra'ila, Ifraimu kuwa ɗan farina ne.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Za su zo da kuka; za su yi addu’a yayinda nake komo da su. Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba, domin ni ne mahaifin Isra’ila, Efraim kuma ɗan farina ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ƙungiyoyin kabilar Ifraimu za su sauka su kafa tutarsu a sashin yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabilar Shugaba Jimilla Ifraimu Elishama ɗan Ammihud 40,500 Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur 32,200 Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni 35,400 Jimilla duka 108,100 Ƙungiyoyin Ifraimu za su zama na uku a jerin.