Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 31:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 31:31
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.


Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.


domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari, ba alkawarin rubutacciyar ka'ida ba, sai dai na Ruhu. Don kuwa rubutacciyar ka'ida, kisa take yi, Ruhu kuwa, rayarwa yake yi.


Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.


Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.


Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa'ad da kuke sha, domin tunawa da ni.”


Sa'an nan ya ce musu, “Wannan jinina ne na tabbatar da alkawari, wanda za a bayar saboda mutane da yawa.


Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.


Saboda haka, shi ne matsakancin sabon alkawari, domin waɗanda aka kira su karɓi dawwamammen gādon da aka yi musu alkawari, tun da yake an yi wata mutuwa mai fansar waɗanda suke keta umarni a game da alkawarin farko.


Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al'amuran ganin ido,


Gama kwanaki suna zuwa sa'ad da zan komo da mutanena, wato Isra'ila da Yahuza. Zan komo da su zuwa ƙasar da na ba kakanninsu, za su kuwa mallake ta,’ ni Ubangiji na faɗa.”


“Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci daga zuriyar Dawuda Wanda zai ci sarauta. Zai yi sarauta da hikima, Zai aikata abin da yake daidai a ƙasar.


Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,


Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa, Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan da nan, Matsewar ruwan inabi kuma Za ta bi bayan shuka nan da nan. Duwatsu za su zubo da ruwan inabi mai zaƙi, Tuddai kuma su gudano da shi.


“Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra'ila da na Yahuza.


Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.


Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba,


Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”


Domin in an sauya matsayin firistoci, sai tilas a sauya Shari'a kuma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ