26 Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.”
26 A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.
Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci, A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya, Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.
Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.”
Ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare.
Zan gan ka domin ni adali ne, Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.