Irmiya 31:12 - Littafi Mai Tsarki12 Za su zo su raira waƙa da ƙarfi, A bisa ƙwanƙolin Sihiyona, Za su yi annuri saboda alherin Ubangiji, Saboda hatsi, da ruwan inabi, da mai, Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu. Rayuwarsu za ta zama kamar lambu, Ba za su ƙara yin yaushi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |