Zan mai da bukukuwanku makoki, In sa waƙoƙinku na murna su zama na makoki. Zan sa muku tufafin makoki, In sa ku aske kanku. Za ku yi makoki kamar iyayen da suka rasa tilon ɗansu. Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.
Ubangiji ya yi tambaya ya ce, “Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, An ci sojojinsu, suna gudu, Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a kowane sashi.”
“Gama ana jin muryar kuka daga Sihiyona cewa, ‘Ga yadda muka lalace! Aka kunyatar da mu ɗungum! Don mun bar ƙasar, domin sun rurrushe wuraren zamanmu.’ ”
Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”
Daga Dan, an ji firjin dawakai. Dakan ƙasar ta girgiza saboda haniniyar ingarmunsu. Sun zo su cinye ƙasar duk da abin da suke cikinta, Wato da birnin da mazauna cikinsa.”
A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.
“Ya mutanena, ku sa tufafin makoki, Ku yi birgima cikin toka, Ku yi makoki mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, Gama mai hallakarwa zai auko mana nan da nan.”