Irmiya 30:18 - Littafi Mai Tsarki18 Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan komar wa alfarwar Yakubu arzikinta, Zan kuma nuna wa wuraren zamansa jinƙai, Za a sāke gina birnin a kufansa, Fādar kuma za ta kasance a inda take a dā. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”
Za a sayi gonaki da kuɗi, a sa hannu a kan sharuɗa, a hatimce su a gaban shaidu, a ƙasar Biliyaminu da wuraren da suke kewaye da Urushalima, da cikin garuruwan Yahuza, da na garuruwan ƙasar tudu, da a garuruwan kwaruruka, da a garuruwan Negeb, gama zan komar wa mutane da wadatarsu a ƙasarsu, ni Ubangiji na faɗa.”