Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 30:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Gama ina tare da kai don in cece ka, Zan hallaka dukan al'ummai sarai, Inda na warwatsa ku. Amma ku ba zan hallaka ku ba, Zan hore ku da adalci, Ba yadda za a yi in ƙyale ku ba hukunci, Ni Ubangiji na faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 30:11
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka tsauta mini, ya Ubangiji, amma da adalcinka, Ba da fushinka ba, don kada ka wofinta ni.


Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”


Gama Ubangiji ya ce, “Ƙasar duka za ta zama kufai, amma duk da haka, ba wannan ne zai zama ƙarshenta na har abada ba.


Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai, Zan kiyaye ka. Ni Ubangiji na faɗa.”


Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.


Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.


domin ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa ka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Zan maishe ka garun tagulla saboda waɗannan mutane, Za su yi yaƙi da kai, amma ba za su yi nasara a kanka ba, Gama ina tare da kai don in cece ka, in kuɓutar da kai.


“Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.


Ku haura, ku lalatar da gonar kurangar inabinta, Amma kada ku yi mata ƙarƙaf, Ku sassare rassanta, Gama su ba na Ubangiji ba ne.


Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini! Kada ka hukunta ni da fushinka!


“Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, Za a kuma sa masa suna Immanuwel.” (Ma'anar Immanuwel kuwa itace Allah na tare da mu.)


Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”


Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku, Na kuwa yi haka saboda yadda nake. Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.


Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.


Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba.


Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.


“‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al'umma.


Ba zan aikata fushina mai zafi ba, Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba, Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Maitsarki wanda yake tsakiyarku, Ba zan zo wurinku da hasala ba.


Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta 'ya'ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”


“Tafi ka faɗa wa Dawuda na ba shi abu uku don ya zaɓi ɗaya wanda za a yi masa daga cikinsu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ