Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 3:6 - Littafi Mai Tsarki

6 A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 3:6
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ƙanwarta kuwa ta ga wannan, amma duk da haka ta fi ta lalacewa saboda kai da kawowa na karuwanci, wanda ya fi na 'yar uwarta muni.


Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’


Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.


Idan sun tuna da 'ya'yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi.


Amma ba su yi biyayya ba, ba su kuma kula ba. Sai suka bi shawarar kansu da ta tattaurar muguwar zuciyarsu. Suka koma baya maimakon su yi gaba.


Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.


A kan dogayen duwatsu masu tsayi kuka sa gadonku. A can kuka haura don ku miƙa hadaya.


Gama su ma sun gina wa kansu wuraren tsafi a tuddai, da ginshiƙai, da gumaka a tuddai, da cikin duhuwar itatuwa.


Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima.


wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,


Gama mutanen Isra'ila da mutanen Yahuza Sun zama marasa aminci a gare ni. Ni Ubangiji na faɗa.”


Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama'ar Isra'ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu.


Har yaushe za ki yi ta shakka, Ya ke 'yar marar bangaskiya? Gama Ubangiji ya halitta sabon abu a duniya, Mace ce za ta kāre namiji.”


Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.


Suna miƙa sadaka a bisa ƙwanƙolin duwatsu. Suna yin hadaya a bisa tuddai, Da kuma a gindin itacen oak, da aduruku, da katambiri, Domin suna da inuwa mai kyau. Don haka 'ya'yanku mata suke karuwanci, Surukanku mata suke yin zina.


Mutanena sun himmantu su rabu da ni, Ko da yake an kira su ga Ubangiji, Ba wanda ya girmama shi.


Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha'inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin.


Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu, Suka zama marasa aminci ga Allah.


Amma ku ku matso nan kusa, ku 'ya'ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa.


Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ