in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba.
“Isra'ila, na yi niyya in karɓe ku kamar ɗana, In gādar muku da kyakkyawar ƙasa Mafi kyau a dukan duniya. Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku, Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba.
Can zan ba ta gonar inabi, In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege. A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta, Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.
Da kuka za su komo. Da ta'aziyya zan bishe su, in komar da su, Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan ruwa, A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba za su yi tuntuɓe ba. Gama ni uba ne ga Isra'ila, Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”
Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka.
Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne mahaifinmu.’ Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka haife mu.’ Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, ‘Ka zo ka taimake mu.’
Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’