Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 3:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ki ta da idonki, ki duba filayen tuddai ki gani, Akwai wurin da ba ki laɓe kin yi karuwanci ba? Kin yi ta jiran abokan sha'anin karuwancinki a kan hanya, Kamar Balaraben da yake fako a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da mugun karuwancinki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani. Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba? A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kin zauna kamar makiyayi a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da muguntarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 3:2
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’ Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace.


Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama.


sai ta tuɓe tufafinta na takaba, ta yi lulluɓi ta lulluɓe kanta, ta zauna a ƙofar Enayim a hanyar Timna, gama ta ga Shela ya yi girma, amma ba a ba da ita gare shi ba.


Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa.


Sai ku hallaka dukan wuraren da al'umman da za ku kora sukan bauta wa gumakansu, a bisa duwatsu masu tsawo, da bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhu.


Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a wurinsa.


Kin ɗauki waɗansu rigunanki, kika yi wa kanki masujadai masu ado, sa'an nan kika yi karuwanci a cikinsu, irin abin da ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a yi ba nan gaba.


“Ku aske gashin kanku, ku zubar da shi. Ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi 'yan zamanin nan, ya rabu da su saboda fushinsa.


An ji murya a kan filayen tuddai, Kūka da roƙo ne na 'ya'yan Isra'ila maza, Domin sun rabu da hanyarsu, Sun manta da Ubangiji Allahnsu.


Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa.


Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da kanka ba, Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba? Ka duba hanyarka ta zuwa cikin kwari, ka san abin da ka yi. Kana kama da taguwa, mai yawon neman barbara.


Sukan laɓe su jira ka kamar mafasa, suna sa mutane da yawa su zama marasa aminci.


(Ba ta jin tsoro, ba ta kuma jin kunya, ko yaushe tana ta gantali a tituna.


Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa.


Ya auri mata ɗari bakwai, dukansu kuwa gimbiyoyi ne. Yana kuma da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa kuwa suka janye zuciyarsa daga bin Ubangiji,


Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’


Suka karkashe mutane marasa laifi, Wato 'ya'yansu mata da maza. Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana, Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.


Ke dai ki yarda da laifinki, Da kika yi wa Ubangiji Allahnki, Kin kuma watsar da mutuncinki a wurin baƙi A gindin kowane itace mai duhuwa. Kika ƙi yin biyayya da maganata, Ni, Ubangiji, na faɗa.


A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.


Gama uwarsu ta yi karuwanci. Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya. Gama ta ce, ‘Zan bi samarina Waɗanda suke ba ni ci da sha, Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ