Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 3:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce, “Ki komo ya Isra'ila, marar aminci, Ni Ubangiji, na faɗa. Domin ni mai jinƙai ne, Ba zan yi fushi da ke ba. Ba zan yi fushi da ke har abada ba, Ni, Ubangiji na faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 3:12
45 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’


Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna, Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.


sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”


Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.


“Ku juyo ku marasa aminci, Zan warkar da rashin amincinku. “To, ga shi, mun zo gare ka, Gama kai ne Ubangiji Allahnmu,


A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.”


Gama ina tare da kai don in cece ka, Zan hallaka dukan al'ummai sarai, Inda na warwatsa ku. Amma ku ba zan hallaka ku ba, Zan hore ku da adalci, Ba yadda za a yi in ƙyale ku ba hukunci, Ni Ubangiji na faɗa.”


amma za su ce, ‘Na rantse da ran Ubangiji wanda ya fito da zuriyar Isra'ila daga ƙasar arewa, daga kuma dukan ƙasashen da ya warwatsa su!’ Sa'an nan za su zauna a ƙasarsu ta kansu.”


Ubangiji ya ce, “Ya mutanen Isra'ila, idan za ku juyo ku komo wurina, Idan kuka kawar da abubuwan banƙyama daga gabana, Kuka kuma bar yin shakka,


Za ka dinga yin fushi da ni? Za ka husata da ni har abada?’ Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi, kin aikata dukan muguntar da kika iya yi.”


Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar ƙauna.


Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara, Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.


A shekara ta uku ta sarautar Hosheya ɗan Ila Sarkin Isra'ila, Hezekiya ɗan Ahaz Sarkin Yahuza ya ci sarautar.


har lokacin da Ubangiji ya kawar da su daga gabansa kamar yadda ya faɗa ta bakin bayinsa, annabawa. Saboda haka aka fitar da jama'ar Isra'ila daga ƙasarsu zuwa Assuriya har wa yau.


kuka sāke komowa wurin Ubangiji Allahnku, ku da 'ya'yanku kuka yi biyayya da maganarsa da zuciya ɗaya, da dukan ranku, bisa ga yadda na umarce ku yau,


Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji, Gama shi ne ya yayyaga, Shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.


“Saboda haka, ni Ubangiji Allah, na ce yanzu zan komo da zuriyar Yakubu daga bauta in nuna mata jinƙai. Zan yi kishi domin sunana mai tsarki.


Ga shi, zan fito da su daga ƙasar arewa, Zan tattaro su daga manisantan wurare na duniya, Tare da su makafi da guragu, Da mace mai goyo da mai naƙuda, Za su komo nan a babbar ƙungiya.


“Ku komo, ya ku mutane marasa aminci, Gama ni ne Ubangijinku. Zan ɗauki mutum guda daga kowane gari, In ɗauki mutum biyu daga kowane iyali, Zan komo da su zuwa Dutsen Sihiyona.


Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar 'yar'uwarta, wato Yahuza, ta gani.


Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa.


Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije, Da girgije kuma zan rufe laifofinka Ka komo wurina, ni ne na fanshe ka.”


Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa'an nan Allah zai yi maka jinƙai.


Amma ƙaunar Ubangiji ga waɗanda suke girmama shi har abada ce. Alherinsa kuwa tabbatacce ne har dukan zamanai,


Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma, Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.


Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji? Har abada ne? Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?


Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”


A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.


In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”


“Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini,


Ba zai yi ta tsautawa kullum ba, Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.


Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuza da titunan Urushalima duka, cewa su ji maganar alkawarin nan, su aikata.


Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.


Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.


“Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.’


“Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra'ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu.


Allah ya ce, “Jama'ar Isra'ila, kun yi mini zunubi, kuna kuwa yin gāba da ni. Amma yanzu ku komo wurina!


“Ki kafa wa kanki alamun hanya, Ki kafa wa kanki shaidu, Ki lura da gwadabe da kyau, Hanyar da kin bi, kin tafi. Ya budurwa Isra'ila, ki komo, Komo zuwa biranen nan naki.


Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ