ya aika wa dukan waɗanda suke zaman talala ya ce, “Haka Ubangiji ya ce a kan Shemaiya mutumin Nehelam, ‘Saboda Shemaiya ya yi muku annabci, alhali ni ban aike shi ba, ya sa ku dogara ga ƙarya,’
Gama sun yi wauta a Isra'ila, sun yi zina da matan maƙwabtansu, sun yi ƙarya da sunana, ni kuwa ban umarce su ba. Ni na sani, ni ne kuma shaida, ni Ubangiji na faɗa.”
“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce a kan Ahab ɗan Kolaya, da Zadakiya ɗan Ma'aseya, waɗanda suke yi muku annabcin ƙarya da sunana. Ga shi, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, zai kashe su a kan idonku.
Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya, Ba su tone asirin muguntarki, Har da za a komo da ke daga bauta ba. Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.