Irmiya 29:7 - Littafi Mai Tsarki7 Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu'a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.