Za su zauna lafiya a cikinta, za su gina gidaje, su yi gonakin inabi. Za su zauna gonakin inabi. Za su zauna lafiya sa'ad da na hukunta maƙwabtansu waɗanda suka wulakanta su. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”
Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.