Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Irmiya 29:32 - Littafi Mai Tsarki

32 saboda haka Ubangiji ya ce, ‘ga shi, zan hukunta Shemaiya, mutumin Nehelam, shi da zuriyarsa ba za a bar masa mai rai ko ɗaya a wannan jama'a ba, wanda zai ga irin alherin da zan yi wa jama'ata, gama ya kuta tayarwa ga Ubangiji,’ ” in ji Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 ga abin da Ubangiji yana cewa, tabbatacce zan hukunta Shemahiya mutumin Nehelam da zuriyarsa. Ba zai kasance da wani da ya rage a cikin wannan mutane ba, ba kuwa zai ga abubuwa alherin da zan yi wa mutanena ba, in ji Ubangiji, domin ya yi wa’azin tawaye a kaina.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Irmiya 29:32
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka, in ji Ubangiji, ‘Zan kawar da kai daga duniya. Za ka mutu a wannan shekara domin ka kuta tayarwa ga Ubangiji.’ ”


Gama yana kama da sagagi a hamada, Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren hamada, A ƙasar gishiri, inda ba kowa.


Haka Ubangiji ya ce, “Rubuta wannan mutum, marar 'ya'ya. Mutumin da ba zai yi albarka a duk kwanakinsa ba. Gama ba wani daga zuriyarsa Da zai gāji gadon sarautar Dawuda, Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”


Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.” Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”


to, ga abin da Ubangiji ya ce maka, ya kai Amaziya, ‘Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe 'ya'yanka a cikin yaƙi. Za a rarraba wa waɗansu ƙasarka, kai kanka kuwa za ka mutu a ƙasar arna. Za a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”


saboda haka Yonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa magaji wanda zai tsaya a gabana ba.’ ”


Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan.


Ba za a binne ka kamar sauran sarakuna ba, saboda ka lalata da ƙasarka, ka karkashe mutanenka. Daga cikin mugayen iyalinka ba wanda zai ragu.


Saboda haka kuturtar Na'aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.” Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.’


Sa, an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.


Zan hukunta shi, shi da zuriyarsa, da barorinsa saboda muguntarsu. Zan kawo dukan masifar da na hurta a kansu, da a kan mazaunan Urushalima, da a kan mutanen Yahuza, amma sun ƙi ji.”


Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.


Masu zunubi daga cikin jama'ata za su mutu a yaƙi, Wato dukansu da suke cewa, ‘Allah ba zai bar wata masifa ta kusace mu ba!’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ