haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. Ga shi, ka aika da wasiƙu da sunanka zuwa ga dukan jama'ar da suke a Urushalima, da zuwa ga Zafaniya ɗan Ma'aseya, firist, da kuma ga dukan firistoci, cewa:
Wannan ita ce maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa Irmiya sa'ad da sarki Zadakiya ya aiki Fashur ɗan Malkiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, wurin Irmiya cewa,
Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila.
Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su.